(ABNA24.com) Sojojin sama Syria sun yi nasarar kakkabo makamai masu linzami da ‘yan sahayoniya su ka harba akan sararin samaniyar Deir-Zur da kuma Suwaida’a.
Majiyar sojan Syria ta ambaci cewa da misalin karfe 12;45 na tsakar daren jiya ne sojojin abokan gaba na Isra’ila su ka kai hari ta sama akan sansanoni daban-daban na sulaimah, da Saburah, da ke Hamat, sai dai nan take dakarun kare samaniyar Syria su ka mayar da martani, tare da yin nasarar kakkabo da dama daga cikinsu.
A can yankunan Deir-Zur da Suwaidah ma dai ‘yan sahayoniyar sun kai wasu hare-haren da su ka yi sanadiyyar shahadar sojojin Syria biyu da kuma jikkata wasu da dama.
Sojojin HKI na yawaita kai hare-hare akan cibiyoyi da sansanonin sojan kasar Syria, tun baarkewar rikicin kasar kusan shekaru 9 da su ka gabata.
/129
25 Yuni 2020 - 05:43
Lambar labari: 1050095
Sojojin sama Syria sun yi nasarar kakkabo makamai masu linzami da ‘yan sahayoniya su ka harba akan sararin samaniyar Deir-Zur da kuma Suwaida’a.